Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 2 Sun Mutu, Sama Da Miliyan 1 Sun Rasa Wuta A Canada


Ruwan Kankara da Iska Mai Karfi Ta Kayar Bishiyoyi a Montreal, Quebec, Canada April 6, 2023.
Ruwan Kankara da Iska Mai Karfi Ta Kayar Bishiyoyi a Montreal, Quebec, Canada April 6, 2023.

Mutane biyu ne suka mutu yayin da sama da miliyan guda suka rasa wutar lantarki a ranar Alhamis, bayan da dusar kankara ta afka wa larduna biyu mafi yawan jama’a a kasar Canada, gabanin hutun karshen mako.

Wannan lamarin dai ya janyo ruwan kankara da sika mai karfin gaske, wacce ta kayar da bishiyoyi da turakun wutar lantaki.

Kimanin mutane miliyan daya basu da wutar lantarki a Quebec da kuma kusa 110,000 a Ontario har zuwa karfe 4 na yammacin ranar Alhamis, a cewar Poweroutrage.com. Idan aka hada daukewar wutar a duka lardunan ya haura akalla miliyan 1.3 a farkon ranar.

Lardunan biyu sun kai fiye da rabin al’ummar Canada kimanin miliyan 39.

Mutane Sama Da Miliyan 1 Ba Su Da Wutar Lantarki in Montreal, Quebec, Canada, April 6, 2023.
Mutane Sama Da Miliyan 1 Ba Su Da Wutar Lantarki in Montreal, Quebec, Canada, April 6, 2023.

Kamfanonin samar da wutar lantarki a lardunan biyu suna aiki don dawo da wutar lantarki, amma ana sa ran za a ci gaba da yin gyare-gyare na tsawon kwanaki, abun da ke nufin mutanen Canada da dama za su shafe karshen mako na Easter a cikin duhu.

Mutum daya ya mutu a Quebec lokacin da bishiya ta fado masa, a cewar Firimiya Francois Legault a wani taron manema labarai, yana gargadin mutane da su kula da wayoyin wutar lantarki da bishiyoyi da suka yi rauni. Wani mutum kuma ya mutu a gabashin Ontario lokacin da wani reshe ya fado masa, kamar yadda kafar yada labarai ta CTV NEWS ta rawaito.

Firai Ministan Canada Trudeau yake magana ya yi amsa tambayoyi a majalisa da ke Ottawa
Firai Ministan Canada Trudeau yake magana ya yi amsa tambayoyi a majalisa da ke Ottawa

Firai Minista Justine Trudeau, wanda aka zabe shi zuwa majalisar dokokin kasar a mazabar Montreal, ya yi tayin bayar da taimakon gwamnatin tarayya idan ana bukata.

“Wannan lokacin mai matukar wahala. Mutane da yawa ba su da wutar lantarki, bishiyoyi suna faduwa, suna cutar da gine-gine da motoci da komai ma, tabbas abin damuwa ne,” abin da Trudeau ya gaya ma manema labarai kenan a kan titi a gundumarsa yayin da ma’akata ke share wata bishiya da ta fado a bayansa.

Montreal na daga cikin wuraren da aka fi fama da bala’in a Quebec, wanda ya kai kusan rabin jimlar wadanda ba su da wuta a lardin da mafi yawa ke magana da Faransanci.

XS
SM
MD
LG