Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Motar Bas Ta Fado Daga Kan Gada, Ta Halaka Mutum 45 A Afirka Ta Kudu


Ma'aikatar sufuri a Afirka ta Kudu ta sanar cewa wata motar bas ta fado daga wata gada kuma ta kama wuta ranar Alhamis, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 45 daga cikin 46 da ke cikin bas din.

Wani yaro dan shekara takwas kadai ne ya tsira kuma an kai shi asibiti da munanan raunuka.

Motar ta taso ne daga makwabciyarta Botswana zuwa Moria a arewacin kasar, in ji wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar.

Bus plunges off cliff
Bus plunges off cliff

“An yi zargin cewa motar ce ta kubuce wa direban, inda ya yi karo da shingayen da ke kan gadar, lamarin da ya sa motar bas din ta fada gadar ta kama wuta,” in ji sanarwar.

An ci gaba da aikin ceto har zuwa cikin dare yayin da aka gano wasu gawarwakin da suka kone kurmus ta yadda ba a iya gane su, wasu kuma sun makale a cikin tarkace ko kuma suka warwatse a wurin da hadarin ya auku.

Hukumomin yankin sun ce motar bas din tana dauke da lambar motar kasar Botswana, amma ana ci gaba da tantance kasashen da fasinjojin suka fito.

Ministan Sufuri, Sindisiwe Chikunga ya je wurin da hadarin ya afku inda ya yi alkawarin za a gudanar da cikakken bincike kan musabbabin hatsarin.

Afirka ta Kudu na daya daga cikin kasashe a Afirka da ke da hanyoyi masu kyau, sai dai tana kuma daya daga cikin kasashe da mummunan hadurra ke faruwa a nahiyar.

Sa'o'i da yawa kafin hadarin, shugaban kasar Cyril Ramaphosa ya yi kira ga 'yan Afirka ta Kudu da su kula yayin tafiya a cikin makon da za a yi bikin Easter.

“Mu yi iyakacin kokarinmu don ganin an yi wannan bikin Easter lafiya,” in ji shi a cikin wata sanarwa.

Motar bas din ta fado ne daga wata babbar gada da ta hada tsaunuka biyu kusa da Mmamatlakala a lardin Limpopo, kimanin kilomita 300 (mil 190) arewacin Johannesburg.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG