Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matatar Mai Mafi Girma A Afirka Ta Fara Aiki Da Nufin Rage Bukatun Najeriya Na Shigo Da Mai


Kamfanin Matatar Mai na Dangote
Kamfanin Matatar Mai na Dangote

Matatar man fetur mafi girma a nahiyar Afirka ta fara aiki a Najeriya, kamar yadda kamfanin ya bayyana, wanda ya kawo karshen tsawon shekaru da aka kwashe ana jiran soma aikin masana'antar.

WASHINGTON, D. C . - Hakan ya sa a yau Litinin manazarta suka ce kan iya bunkasa aikin tace man a yankin da ya dogara kacokan kan albarkatun man da ake shigowa da su daga kasashen waje.

Aliko Dangote
Aliko Dangote

Matatar man ta Dangote da kafa kan dalar Amurka biliyan 19, tana da karfin samar da gangar mai 650,000 a kowace rana, kuma tuni ta soma fitar da man gas da man jiragen sama, kamar yadda kamfanin na Dangote ya bayyana a ranar Assabar. Ya kara da cewa, a matsayin matatar mai mai zaman kanta ta farko a Najeriya, wani "muhimmin sauyi ne ga kasarmu."

Najeriya na daya daga cikin kasashen da ke kan gaba wajen hako gurbataccen mai a Afirka amma tana shigo da man da aka tace domin amfanin ta na cikin gida. Bangaren mai da iskar gas na kasar ya kwashe shekaru da dama yana fadi-tashi, kuma galibin matatun mai na gwamnati suna aiki kasa da iya karfin su saboda rashin kulawa.

Kamfanin Dangote
Kamfanin Dangote

Kamfanin ya bayyana ta a matsayin babbar matata daya tilo mai zaman kanta mafi girma a duniya, mallakin hamshakin attajirin Afrika, dan Najeriya Aliko Dangote. Tana bayan garin birnin Lagos, cibiyar tattalin arzikin Najeriya, inda take aiki tare da kamfanin takin zamani.

Ana sa ran kamfanin zai samar da kashi 100% na buƙatun Najeriya na man fetur, man gas, kananzir, da kuma man jiragen sama idan ya soma cikakken aiki, in ji Dangote a bara lokacin da aka buɗe kamfanin. Aƙalla kashi 40% na albarkatun man da aka tace, za'a iya fitar da su a wajen kasa, in ji kamfanin.

Matatar Mai A Najeriya
Matatar Mai A Najeriya

Kamfanin ya samu kusan ganga miliyan 6 na danyen mai ya zuwa yanzu daga kamfanin mai na Najeriya, NNPC domin fara aikinsa, duk da cewa zai iya daukar watanni kafin matatar ta kai cikakken karfin aikin ta, kamar yadda manazarta suka bayyana.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG