Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kannywood: Ana Jimamin Rasuwar Jarumin Wasan Barkwanci Kamal S. Aboki


Marigayi Kamal S. Aboki
Marigayi Kamal S. Aboki

Kamal, wanda ya yi fice a fannin wasan barkwanci a shafukan sada zumunta musamman Instagram, ya rasu ne bayan hatsarin mota da ya rutsa da shi.

Masana’antar Kannywood da ke arewacin Najeriya da masoya wasan barkwanci na jimamin mutuwar Kamal S. Aboki wanda ya rasu a ranar Litinin.

Kamal, wanda ya yi fice a fannin wasan barkwanci a shafukan sada zumunta musamman Instagram, ya rasu ne bayan hatsarin mota da ya rutsa da shi.

Mujallar fim, ta ruwaito cewa hatsarin ya auku ne yayin da jarumin yake kan hanyarsa ta komawa Kano daga Maiduguri.

Tuni dai aka mamaye shafukan sada zumunta da ta’aziyyar matashin jarumin, wanda dan asalin Maiduguri ne amma mazaunin Kano.

“Allah ya jikan ka da Rahama @kamal_aboki. Amin.” In ji Ali Nuhu.

Mawaki Salim Smart ya ce, “Allah ya jikan ka Kamal Aboki, ya sa karshen wahalar kenan, ya kyautata makwancin.”

“Inna lillahi Wa’inna ilaihhi Raji’un. Abokina Allah ya jikan ka da Rahama. Allah ya gafarta maka.” Real_adamsdorayi ya rubuta.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG