Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aurena Da Sheila Ya Kare – Israel DMW


Israel, dama, da Davido, hagu (Hoto: Instagram/Israel DMW)
Israel, dama, da Davido, hagu (Hoto: Instagram/Israel DMW)

A wani dogon sako da ya wallafa a shafin Instagram a ranar Asabar, Israel ya yi wasu zarge-zarge akan matarsa Sheila.

Israel Afeare, daya daga cikin hadiman mawaki Davido ya sanar da mutuwar aurensa.

Israel, wanda aka fi sani da Israel DMW, ya bayyana yadda aurensa da Sheila yake fuskantar matsaloli iri-iri.

A watan Oktoban shekarar 2022 Israel da Sheila suka yi aure.

A wani dogon sako da ya wallafa a shafin Instagram a ranar Asabar, Israel ya yi zarge-zarge akan matarsa Sheila.

Israel ya zargi Sheila da yarda ta auresa saboda ta ga yana da kudi. Ya kuma zarge ta da yin amfani da tauraruwarsa wajen gudanar da harkokinta.

A ranar Juma’a Sheila ta zargi Israel da yunkurin kuntata mata inda ta ce duk abin da ya same ta ko iyalanta Israel ne.

Dandalin Mu Tattauna

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG