Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministar Al’adu Ta Nemawa Zack Orji Taimako, Ta Bayyana Cewar Anyi Masa Tiyata A Kwakwalwa


Ministar Al'adu Hannatu Musawa
Ministar Al'adu Hannatu Musawa

Ministar Fasaha, Al’adu da Bunkasa Tattalin Arziki ta Hanyar Kirkira, Hannatu Musawa, ta bayyana cewar an yiwa jarumin masana’antar Nollywood dake jinya, Zack Orji tiyata a kwakwalwarsa a wani asibitin da aka maida shi daga babban asibitin kasa.

Ministan ta bayyana hakan ne sa’ilin data ziyarci asibitin dake abuja a ranar talata.

A cewarta takai ziyarar ne domin tallafawa shahararren jarumin, da yi mishi fatan samun sauki tare da mika sakon fatan alkhairi daga gwamnatin tarayya ga shi da iyalansa.

“Wannan bawan all.h ya sadaukar da lokaci da basira domin ya samu dariya da nishadantar da ‘yan Najeriya tsawon lokaci.

“Yana daga cikin mutanen da suka aza harsashin ginin masana’antar fina-finan Najeriya kuma gashi an yi rashin sa’a yana fama da kalubale na lafiya harma anyi mishi tiyata a kwakwalwa.

“Iya abinda zamu iya yi a matsayinmu na gwamnati shine bashi tallafin da ya dace domin tabbatar da ya samu waraka cikin sauri”, in ji Ministan.

Ta kara da cewa “tiyatar kwakwakwa abu ne mai wahalar gaske, don haka yana da mahimmanci a "matsayi na ta Ministar Fasaha, Al’adu da Bunkasa Tattalin Arziki ta Hanyar Kirkira in ziyarce shi”, in da ta bukaci ‘‘yan najeriya su taimaka mishi da addu’a da duk abinda za su iya domin tallafa masa da iyalinsa wajen ceto rayuwarsa”.

Musawa ta ci gaba da cewar gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu ta fahimci mahimmacin da fannin fasaha ke da shi wajen bunkasa tattalin arzikin kasa, kuma ta dukufa wajen tabbatar da walwalar masu ruwa da tsaki a harkar.

A cewarta, ma’aikatar raya al’adu karkashin kulawarta na aiki tukuru wajen bijiro da shirye-shirye da tsare-tsaren tabbatar da jin dadin masu ruwa da tsaki a fannin.

Musawa, wacce ta bada gudunmowar adadin kudin da ba’a bayyana ba domin biyan kudin asibitin jarumin dake jinya, tace akwai kyakkyawan fata a fannin kirkira da fasahar Najeriya.

“Guda da ga cikin mahimman abubuwan da muka bijiro da shi a ma’aikatarmu shi ne tabbatar da walwalar, ba wai ga iya jaruman da suka yi shura ba, harma da ilahirin mambobin masana’antar shirya fina-finan”.

Rahotanni sun bayyana cewar an kwantar da Zack Orji mai shekaru 64 a sashen Kulawar Musamman na Asibitin Kasa dake Abuja bayan da ya yanke jiki ya fadi a jajibirin sabuwar shekara, kafin daga bisani a maida shi zuwa wani asibiti mai zaman kansa.

Dandalin Mu Tattauna

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG