Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Allah Ya Yiwa Samanja Jarumin Fina Finan Hausa Rasuwa


Veteran Hausa actor, Usman Baba Pategi, popularly known as Samanja Mazan Fama
Veteran Hausa actor, Usman Baba Pategi, popularly known as Samanja Mazan Fama

Allah ya yi wa fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Usman Baba Pategi, wanda aka fi sani da Samanja Mazan Fama rasuwa yana da shekaru 84 a duniya.

Shahararren jarumin Kannywood mazaunin Kaduna ya rasu ne da misalin karfe 12:15 na safe a ranar Lahadi 12 ga watan Nuwamba.

Daya daga cikin ‘ya’yan marigayin, Mohammad Usman, shine tabbatar da rasuwarsa, inda ya bayyana cewa ya bar mata biyu da ‘ya’ya 12.

Har yanzu dai ba a bayyana musabbabin rasuwarsa ba kamar yadda dansa ya ce an yi sallar jana'izar ne a wani masallaci da ke Kabala Costain a Kaduna.

Usman ya shahara a shirye-shiryen talabijin tun cikin shekarun 1980, wanda ya saba da sunan Samanja.

Usman ya kasance tsohon jarumin fina-finai kuma tsohon jarumin yaki, wanda ya yi yakin basasar Najeriya a karkashin marigayi tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Sani Abacha, wanda a lokacin yana karamin matsayi.

Dandalin Mu Tattauna

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG